Min menu

Pages

latest news

Allah Sarki Natasa Akpoti.🥺

 Allah Sarki Natasa Akpoti.🥺👇👇👇👇😭



Wanda bai ji bari ba Dole zaiji Hoho, lokacin da shugaban majalisar Dattawa ya baiwa Natasha haƙuri, inda babu wata manufa da takeyin abin domin sa da sai tayi haƙuri, amma bayan ya fito a idon duniya ya bata haƙuri sai ya zamo kamar ma ya ƙara zuga ta ne. 


1. Dakatar da ita na tsawon watanni 6.


2. Dole ta rubuta takardar neman afuwa kafin ta dawo bakin aiki.


3. Dakatarwar ta fara aiki daga 6 ga Maris.


4. An kulle ofishinta har tsawon lokacin dakatarwar, tare da mika dukiyar gwamnati.


5. Kar ta kusanci harabar majalisar dokoki ta kasa (NASS).


6. An dakatar da albashinta, alawus-alawus da jami’an tsaronta.


7. An hana ta bayyana a matsayin Sanata a kafafen yada labarai na cikin gida da na duniya.


Wannan shine sakamakon abin nan da Bahaushe yake cewa inda rabon Asha duka bari bata maganin komai, abinda Natasha tayi abune da ya taɓa kimar majalisar Dattawa.

Comments