Min menu

Pages

latest news

KAFTIN AHMED MUSA YA GWANGWAJE WASU MUTUNE (4) DA KYAUTAR GIDAJE A BIRNIN TARAYYA ABUJA, CIKI HAR DA MAI GADINSA

 

Kai Tsaye Latsa Wan Nan Hoton Na Kasa Yanzu Ka Kalli Cikakken Bidiyon Aciki๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡



A ฦ™oฦ™arin da ya saba yi wajen tallafawa al'umma, shahararren ษ—an ฦ™wallon ฦ™afan Najeriya, Kaftin Ahmed Musa MON ya gwangwaje wasu mutane da kyautar gidaje domin su samu muhallin zama da iyalansu.


Daga cikin mutanen da suka samu gidan akwai mai gadinsa wanda ya ba shi gida mai ษ—aki ษ—aya, da P.A ษ—insa wanda ke zaman abokinsa shi ma ya samu gida mai ษ—aki uku, da kuma ma'aikacin ฦ™ungiyar ฦ™wallon ฦ™afa shi ma ya samu kyautar gida mai ษ—aki uku, sai kuma wata ฦดar Jarida wacce suka daษ—e tare tun yana ฦ™ungiyar ฦ™wallon ฦ™afa ta Kano Pillars, ita ma ya gwangwaje ta da gida mai ษ—aki biyu.


Kaftin Ahmed Musa mutum ne gwarzo wanda ya daษ—e yana sanya farin ciki da walwala a cikin zukatan al'umma daban-daban. Ko da a baya-bayan nan ya gwangwaje tsohon ษ—an wasan Hausan nan Baba Karkuzo da kyautar gida, ya kuma sanyawa wasu abokansa tun na ฦ™uruciya gida kyauta ya ba su. Akwai mutane da dama da suka rabauta da samun gida a sanadiyyarsa, wasu kuma ya tallafa musu ne ta fuskar ilimi, abinci da jarin dogaro da kai da dai sauran muhimman fannoni rayuwa daban-daban. Wanda a sanadiyyar hakan ษ—umbin al'umma na cigaba da yi masa godiya da addu'ar fatan alkhairi.

Comments