GWAMNATIN JIHAR ZAMFARA TA MAYAR DA MARTANI KAN AIKIN FILIN JIRGIN SAMAN JIHAR
A cewar gwamnatin Jihar Zamfara, aikin filin sauka da tashin jiragen sama da ta gada, ko kusa bai kai ga kusan kammaluwa ba a lokacin da ta gaji gwmnati a hannun tsohon gwamna Matawalle.
Tunda farko a martanin da ya maida, tsohon gwamnan Jihar, Bello Matawalle ya bayyana cewa sun cimma kusan kaso 90 na aikin kafin su bar mulki, iƙirarin da gwamnatin Dauda Lawal ta musanta.
A cewar gwamnatin Dauda Lawal, ba za ta ɗora laifin ƙin kammaluwar aikin a kan kowa ba, amma dai za ta yi iya ƙoƙarinta ta kammala shi saboda amfanin al'ummar Jihar.
Aikin filin sauka da tashin jiragen sama (Cargo) na Jihar Zamafara, aiki ne da ya haifar da ruɗani da cece-ku-ce tsakanin tsohuwar gwamnati da gwamnati mai ci a Jihar.
Tsohon gwamnan Jihar, Bello Matawalle shi ne ya ƙirƙiri aikin shekarun baya lokacin ya na gwamna da manufar magance matsalar rashin tashi da saukar jiragen sama a Jihar, wanda a tarihin Jihar Zamfara ba ta da filin jirgin sama tun da aka ƙirƙiri Jihar a 1996.
Tun bayan shigarsa Ofis a matsayin gwamna a shekarar 2023, matakin da aikin ya ke ciki ya ke cigaba da tayar da ƙura bisa zargin fidda maƙudan kuɗaɗe da sunan kammala aikin.
Gwamnatin Dauda Lawan ta bayyana cewa iƙirarin da tsohuwar gwamnati ke yi cewa aikin ya kai kaso casa'in ba gaskiya ba ne.
Sai dai a cewar gwamnatin ba za ta zargi kowa ba, amma dai za ta yi ƙoƙarin kammala shi domin al'ummar Jihar su amfana.
Mista Agigi ya kuma musanta zargin cewa gwamnati mai ci ta lalata wasu tituna waɗanda aka gina a kan kuɗi kusan Naira Biliyan Huɗu.
Ya kuma ƙara da cewa gwamnatin Dauda Lawal za ta cigaba da aikin jirgin saman dazarar ta kammala gudanar da bincike a kai.
Tsohon gwamna Matawalle wanda shi ne ministan tsaro a yanzu, ya musanta dukkan wasu zarge-zarge da ake masa kan aikin tashar jirgin na (Cargo) cikin hira da manema labarai.

Comments
Post a Comment