Min menu

Pages

latest news

ƙarancin albarka akan Dukiya da kayan abinci da kuma rayuwa gaba ɗayanta.

 

Mutane da yawa cikin wannan lokacin suna ƙorafi akan ƙarancin albarka akan Dukiya da kayan abinci da kuma rayuwa gaba ɗayanta.


Mafi girman abin da ya haifar da haka shi ne yadda mutane suke wasa d kuma sakaci wajen mu'amala d dukiyar Haram. Dukiyar Haram babban sababi ce wajen ɗaukewar albarka a rayuwa.


Mafi yawan mutane suna ɗaukan cewa, wanda ya tare ka ya ƙwaci kuɗinka ko ya haura gidanka ko ya fasa shagonka dss sune kaɗai masu cin Haramun.


Suna mantawa da:


1. Akwai wanda yake cinye gadon marayu ko kuma  ya cinye dukiyar gado ta matarsa ya hana iyayenta haƙƙin da Allah ya basu.


2. Cin hanci da Rashawa duk sun zama jiki har an daina jin kunya ma wajen kar'bar su.


3. Aikin gwamnati d aka ɗauke ka baka sauke abin aka ɗora maka na haƙƙi ba. Wasu sai ranar d suka ga dama, a lokacin d suka ga dama suke zuwa aiki.


4. Leburan da aka ɗauka aiki amma ya yi ha'inci a wajen aikin ko kuma siyan kayan aikin.


5. Kayan d ka sayar ba tare da ka bayyana aibunsu ba.


6. Ɗan kasuwar da bai san Halal da Haram ba.


7. Bashin da ka kar'ba da niyyar ba zaka biya ba.


8. Taurin bashi a lokacin da kake da wadata.


9. Dukiyar Riba da kake mu'amala da ita.


10. 'Boye kayan abinci da niyyar su yi tsada


11. Wanda ya amince maka, ya aikeka domin siyo masa wani abu, kai kuma ka ƙara masa kuɗi haka kawai.


12. Malamin da yake fatawa saboda neman duniya


Da dai sauransu cikin abubuwa da muke aikatawa amma kuma muke ganin ba laifi ba ne. 


Waɗannan da  ire-irensu sune suka jawo ɗaukewar albarka a cikin rayuwarmu. Sune manya-manyan sababan d suka jawo Azzaluman shugabanni suke mulkar mu.



أنت الآن في المقال الأخير

Comments